DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.56     |Issue 1 | April 2025|

Hauwa Rabi’u Ɗanbappa 

Hauwa Tanko Idris 


Tsakure.

Kiɗa da waƙa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza wanda aka yi wa ko ta kai shi ta baro ko kuma ta ƙara masa karsashi har ya cimma gaci musamman a kiɗan maza. Adon harshe salo ne daga cikin salalan da makada kan yi amfani da shi wajen kwarzanta iyayen gidansu da kambamasu da ƙoƙarin dakushe farin jini da ƙima ta abokan hamayya. Wannan takarda ta bibiyi wasu daga cikin adon harshe a waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi domin fito da irin na sa salon, na yi wa waƙoƙinsa ado da kwalliya da kwarzanta iyayen gidansa da muzanta abokan adawa. An yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (2003). Sannan an yi amfani da nau'in bincike bi sharhi wajen kalailaice bayanan wannan takarda. Takardar ta bibiyi wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi musamman waɗanda ya yi wa 'yan farauta da ‘yantauri da ɓarayi, ta kuma gano yadda Makada Kassu Zurmi ya ke amfani da salon adon harshe domin nuna gwanintar harshe. Haka kuma ta gano ya na kuma amfani da salon adon harshe irin su jinsintarwa da siffantawa da salon kambame da kamantawa na daidaito da fifiko ko kuma na kasawa duk a cikin waƙoƙinsa. Ta kuma gano cewa Makaɗa Kassu ya nakalci harshen Hausa, wannan ya ba shi dama wajen yi wa waƙarsa ado da kwalliya. Adon harshe, Kassu Zurmi,kamantawa, jinsirtarwa, alamtarwa kambam