DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.47 |Issue 1 | April 2025|
Shu’aibu Abdullahi Jangebe
Sashen Hausa Kwalejin Kimiya Da Fasaha Gusau, Jihar Zamfara
Tsakure
Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da ake aiwatarwa don ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gudummawa ta musamman. Kusan kiɗa ya yi ruwa, ya yi tsaki sosai a cikin rayuwar Bahaushe, musamman rayuwar da ta dangane da zamantakewa da sana’o’i da bukukuwa da lokutan shaƙatawa. Akwai waƙoƙin baka da yawa waɗanda suka danganci fuskoki daban- daban tun daga na farauta da yaƙe- yaƙe da na sarakuna da na masu sana’o’in gargajiya da na ‘yan kasuwa wato attajirai da na masu jaruntaka da na sojoji da na ma’aikatan gwamnati ko wata Hukuma da na Malamai bisa fannoninsu mabambanta da na dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da gulabe da garuruwa har zuwa ga waƙoƙin yunwa da fari da na ɓarayi da na ‘yan caca da na soyayya da sauransu. Ashe ke nan waƙoƙin baka na Hausa sun yi ruwa da tsaki a ko’ina cikin ɓangarorin rayuwar Hausawa.