DOI: 10.65760/kassu.i1.2 |Issue 1 | April 2025|
Aminu Alhassan Idris1, Nuhu Abbullahi Jibril2, Aisha Abdulrahaman Alfanda3
1Department of Nigeria and Linguistics, Kaduna State University, Kaduna. (KASU)
2Ƙaramar Hukumar Kura ta Jihar Kano. Ɗalibi a Jami’ar Bayero Kano (Ph.D Hausa)
3Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, Kano
Tsakure
Hausawa suna da nau’in magunguna na gargajiya, wanda suke amfani da suke domin kawar da wata cuta da ta addabi mutum. Magungunan Hausawa suna da ɓangarori iri-iri daban-daban.wajen yin amfani da su. Mafarauta da `yan tauri a ƙasar Hausa suna amfani da magunguna na gargajiya domin kare kansu daga abokan gaba ko shuhura ko tsare kai daga faɗawa cikin haɗura na abokan gaba, wani lokaci ma har maganin ƙarfe da dabbobi na dawa. Irin waɗannan magunguna ana amfani da saiwowi ko ganyayyaki ko kauci ko wasu sassa na jikin wasu dabbobi. Makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa musamman Kassu Zurmi yana amfani da salon ambaton magunguna na gargajiya da mafarauta da`yan tauri suke amfani da su. Manufar wannan takarda ita ce fito da magunguna na gargajiya da mafarauta da `yan tauri da suke amfani da su. Sannan wannan takarda za ta yi amfani da ra’in Ma-yi-ma-gani, wato (Therory of Trial and Error) Edward Lee Theradile ne ya ƙirƙiro shi a shekarar 1979. Haka kuma, wannan takarda za ta yi ƙoƙarin bibiyar waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda suke ƙunshe da waɗanan magunguna na gargajiya ta hanyar sauraron waƙoƙin a MP3 da bibiyar rubutattun waƙoƙinsa da mazarta da suka yi. Daga ƙarshe ana sa ran wannan takarda za ta gano duk waɗansu magungunan gargajiyar da Kassu Zurmi ya ambata a cikin wasu waƙoƙinsa.