DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.18 |Issue 1 | April 2025|
Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji Inkiya:Fadar Mai Martaba Ɗan’alin Birnin Magaji, Birnin Magaji, Jihar Zamfara,
Tsakure
Idan ana neman makaɗin maza wanda in ka ayyana manyan sana’o’in jaruntaka to sai an ambaci sunansa a matsayin makaɗin waɗannan sana’o’i kafin a ambaci sunan kowa in dai a zamaninsa ne. Ayyuka a kan Kassu Zurmi sun gabaci wannan maƙala inda ƙumshiyarsu ta ayyana Kassu ya yi zarra ta fuskar waƙa. A wannan tsakure za a sake kallon wani yanayi da Kassu ya yi bajinta a fagen Farauta. Yadda Kassu ya koɗa wasu mafarauta suka nuna bajintarsu a fagen farauta. Idan ana maganar farauta a yankin da Kassu ya fito, haƙiƙa waƙoƙin Kassu sun taimaka wa mafarauta samun nasarar aje tarihi a wannan sana’a ta farauta. An saurari waƙoƙin da aka kalato, an kuma tattauna da waɗanda suka halarci farautar da Kassu ya waƙe da kuma darussan da waƙar ke koyarwa ga al’umma masu sauraren waƙoƙin Kassu. Kodai akwai kambamar zulaƙe a cikin labartawar wannan waƙa, gurmuzun da ya gina wannan waƙa ya naɗe tarihi da al’adun bajinta na al’ummar Hausawa