DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.9 |Issue 1 | April 2025|
Hadiza Farouk Abba
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano
Tsakure
Waƙoƙin baka na Hausa cike suke da dabarun jawo hankali. Wannan ya sa a kodayaushe za a ga waƙoƙin suna cike da armashi da salo mai ban-sha'awa. Gusau (2003 da 2023) ya kira waɗannan dabaru da adon harshe. Ɗangambo (2007) yana ambaci waɗannan dabaru da dabarun salon sarrafawa. Abba da Zulyadaini (2011) sun kira su da dabarun fitar da salo. Haka kuma Auta (2017) ya kira su da dabarun jawo hankali. Ashe kenan, dabarun jawo hankali wani reshe na salo da makaɗan baka na Hausa suke amfani da shi wajen isar da saƙonni iri daban-daban a cikin waƙoƙinsu. Babbar manufar wannan takarda ita ce yin nazarin dabarun jawo hankali na kwatantawa da jinsintarwa da siffantawa da kuma alamtarwa a cikin Ɗiyan wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi. An ɗora wannan takarda a kan ra'in Waƙar Baka Bahaushiya na Gusau (2003, 2014 da 2023). An yi amfani da dabarar bincike bi-bayani wajen fito tare da sharhantar ɗiyan waƙoƙi masu ƙunshe da wannan salo ma dabarun jawo hankali. Takardar ta gano cewa Kassu Zurmi ya fi yin amfani da dabarar mutuntarwa a cikin waƙoƙinsa sama da kowace dabara ta jawo hankalin mai sauraron.
Fitilun Kalmomi: Dabarun Jaho Hankali, Waƙa, Kassu Zurmi