DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.22   |Issue 1 | April 2025|

Nura Lawal,  Ahmad Magaji  

Department of Nigerian Languages, Bayero, University, Kano

Tsakure

Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace  yanayin dangantakar ‘yantauri da sarauta da masaurata a wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa. Haka kuma, an yi amfani da hanyar nazarin waƙar baka Bahaushiya, wato (Gusau,2023) domin yin gajoranci wajen ƙalailece misalan wannan nazarin.  Har ila yau, hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun  haɗa da sauraren wasu waƙoƙin kai tsaye a  MP3 sannan aka juyar da su a rubuce kuma tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga Diwanin Waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2009 da 2014), da kuma littafi mai ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi, wato (Magaji, 2016) da Kundin Ƙaura (2017). Har wa yau, an yi amfani da hanyar  bi-sharhi, wato (}ualitative Research). A wannan takarda an fahimce, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar masu sarauta da ‘yantauri a tsarin zamantakewar al’umma Hauswa, musamman a kan abin da ya shafi gudanar da mulki irin na sarauta a kowa ne mataki. Har ila yau, an lura, a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi an nuna yadda kyakkyawar dangantaka take tsanin masu sarauta da ‘yantauri, musamman ta fuskar samar da tsaro da kuma bayar da kariya ga masarauta da masu sarauta da kuma tabbatar da hukunci. Sannan kuma an lura ‘yantauri mutane masu nuna jajircewa da juriya da kuma kuri don tsoratarwa. Wanda hakan ta sa kusan kowane mai sarauta, musamman mai gunduma yake da sarkin tauri.