DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.19    |Issue 1 | April 2025|

Halima Ahmad Umar 

Tsangayar Fasaha, Shashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar Sakkwato

Tsakure 

A kowane lokaci, mai neman nazarin wani abu na al’ada idan ya ratsi waƙoƙin baka na Hausa, yakan ji shi warkal irin na wanda ya shiga rijiya da dawonsa. Buƙatar wannan nazari ne ya dubi hoton faɗi-tashin auren Bahaushe a waƙar Makaɗa Abubakar Kasssu Zurmi wadda ya rera wa tauraronsa mai suna Shayi Ɗangidan Labbo. Nazarin ya yi ƙoƙarin dubin wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar masu alaƙa da shi a matakan ilimi daban-daban. An yi hakan ne saboda a gano giɓin da magabata suka bari, saboda a san yadda za a cike shi. An yi ƙoƙarin yin amfani da hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da, sauraron waƙar Shayi Ɗangidan Labbo daga bakin wanda ya rera ta  a cikin na’urar adana bayanai ta memori. Haka kuma, an yi ƙoƙarin karanta waƙar a cikin rubuce-rubucen wasu masana da suka taskance ta. Baya ga haka, binciken bai  yi ƙasa a guiwa ba wajen tuntuɓar masana al’adun aure na Hausawa da kuma waɗanda suka fahimci waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi. An yi wa aikin farfajiya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo kaɗai, domin kada a wuce makaɗi da rawa. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya bayyana sun haɗa da: Binciken ya gano yadda Makaɗi Kassu Zurmi ya fitar da wasu ɗabi’u da halaye mara kyau ga masu neman aure waɗanda idan ba a kula da su ba a wajen zaɓin miji za su zama ƙalubale ga rayuwar ma’aurata. Wannan ya tabbatar da gudummuwar da makaɗin ya bayar wajen bunƙasa al’adun Hausawa. Haka kuma, nazarin ya gano cewa,  makaɗa ya yi wa iyaye hannunka-mai-sanda  musamman a wajen bayar da ɗiyarsu aure don gudun kada a faɗa hannun bara-gurbi.

Keɓaɓɓun Kalmomi:  Faɗi-tashi, Aure da kuma Bahaushe