DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.14    |Issue 1 | April 2025|

Hassan Muhammad 

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar Sakkwato

Tsakure Tsakure 

Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da hikimomi wajen tsara zantuttukan hikima a cikin baitocin waƙa ko ɗiyan waƙa. Wannan baiwa da Allah ya yi musu ya sa ake tsintar abubuwa nagartattu da yawa waɗanda suka shafi hanyoyin rayuwar al’umma a cikin waƙoƙinsu. Da ma shi harshe sha-kundum ne a rayuwar kowace alumma domin shi ke bayyana kowane irin alamari da zai fito cikin alumma musamman fasahohinsu na baka. A dalilin haka ne aka shirya wannan maƙala da aka yi wa take da Gurbin Musulunci a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi. Wannan maƙala ta ƙudiri fito da wasu abubuwa da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan wasu waƙoƙinsa da ya yi, waɗanda nazari ya gano cewa ko shakka babu abubuwan an ambace su ne a dalilin tasirin da addinin Musulunci ya yi a rayuwar mawaƙin. An zaɓi waƙoƙi biyu daga cikin waƙoƙin da mawaƙin ya yi domin fito da ƙudirin maƙalar. Waƙoƙin su ne Waƙar Iro Shayi ɗan gidan Labbo’ da ‘Waƙar Malam Sanda ɗan Ruhwa’i’.