DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.23    |Issue 1 | April 2025|

Sakina Adamu Ahmad   

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya., Jami’ar Jihar Sokoto


Tsakure 

Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da aka aiwatarwa domin ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gudummuwa ta musamman. Kusan a ce kiɗa ya yi ruwa ya yi tsaki, ya durmiya sosai a cikin rayuwar Bahaushe, musamman rayuwar da ta danganci zamantakewa da sana’o’i da bukukuwa da lokutan shaƙatawa. Akwai waƙoƙin baka da yawa waɗanda suka danganci fuskoki daban- daban tun daga na farauta da yaƙe- yaƙe da na Sarakuna, da na masu sana’o’in gargajiya da na ‘yan kasuwa wato attajirai da na masu Jaruntaka da na Sojoji da na ma’aikatan Gwamnati ko wata Hukuma da na Malamai bisa fannoninsu mabambanta da na dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da gulabe da garuruwa har zuwa ga waƙoƙin yunwa da fari da na ɓarayi da na ‘yan caca da na soyayya da sauransu. Ashe ke nan waƙoƙin baka na Hausa sun yi ruwa da tsaki a ko’ina cikin ɓangarorin rayuwar Hausawa. Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen rayuwa ta mutum da kuma Al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan jibge cikin waƙoƙin baka na Hausa. (Gusau, 2014). Alhaji Kassu Zurmi yana ɗaya daga cikin mawaƙan baka na Hausa, wanda Allah ya bashi basira da hazaƙa da fasaha da hikimar naƙaltar harshen Hausa da adabi da abin da ya shafi al’adun Hausawa tun daga sana’a da muhalli da haihuwa da kuma sunayen abubuwa na dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da ke cikin duniya baki ɗaya. Wannan muƙala za ta dubi gurbin muhalli na Dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da ke cikin wasu waƙoƙin Kassu Zurmi. Kuma za a kawo taƙaitaccen tarihin shi mawaƙin, da kuma nuna hanyoyin da aka bi domin tattara wannan bincike da aka yi. Haka kuma, muƙalar za ta kawo sakamakon binciken da kuma kammalawa daga ƙarshe.