DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.4 |Issue 1 | April 2025|
Aminu Ibrahim
Sashen Harsunan Nigeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Tsakure
Babbar manufar maƙalar ita ce fito da sana’o’in gargajiya na Hausawa, waɗanda Kassu Zurmi ya taskace a cikin waƙoƙinsa tare da duban yadda shi makaɗin ya kalle su a cikin waƙoƙinsa, kuma a fito da gudummuwar da suke bayarwa wajen inganta tare da bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa. An yi ƙoƙarin fito da dangantakar da sana’o’in da aka ambata a cikin waƙoƙin suke da shi da kuma yadda hakan yake samar da kyakkyawan yanayi na cuɗanni-in-cuɗe-ka a tsakanin sana’o’in na gargajiya. An yi amfani da hanyoyi da dama wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen gina wannan maƙala. Hanyoyin sun haɗa da, yin hira da masana, musamman na waƙoƙin baka da nazarce-nazarcen littattafai da kundayen da magabata suka rubuta a kan waƙoƙin Kassu Zurmi. Har wa yau, an saurari waƙoƙinsa da aka naɗa a faya-fayen sidi na rediyo da na talabijin. Binciken ya gano yadda Hausawa suka ɗauki sana’o’insu na gargajiya da daraja, kuma abin dogarau wajen neman na kai da kare mutunci. Haka kuma, Hausawa na matuƙar alfahari da sana’o’insu na gado, kuma suna kare martabarsu a duk inda suka samu kan su ba tare da jin tsoro ko fargaba ba.