DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.41 |Issue 1 | April 2025|
Aishatu Yahaya Tambuwal
Sashen Hausa, KwalejinIlimi Ta Shehu Shagari, Sakkwato.
Tsakure
Waƙawani ɓangare ne na adabin Hausa wadda kuma hanya ce da akan yi amfani da ita wajen gina tunanin al’umma da fahimtar da su wasu hanyoyin gudanar da rayuwarsu. Dabarun isar da saƙonni ta hanyar amfani da waƙa suna da matuƙar yawan gaske. Wannan shi ya samawa ƙasukanyi amfani da hanyoyi iri daban-daban domin isar da saƙonninsu. Wannan maƙalar za ta kalli waƙoƙin makaɗin nan mai suna Kassu Zurmi, da irin yadda yakan yi amfani da habaici wajen gabatar da waƙoƙinsa. Kyakkyawan nazari da sauraron waƙoƙinsa su ne hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan maƙalar. Sannan kuma an yi amfani da ra’i wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi ko kyallaro al’adun al’umma kamar yadda Ado (2017:87) ya bayyana wajen gudanar da maƙalar. A ƙarshen wannan maƙalar, za a fahimci cewa mawaƙi Kassu Zurmi ya ƙware matuƙa wajen amfani da habaici a cikin waƙoƙinsa wanda wani ɓangare ne na adabin Hausa.