DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.27 |Issue 1 | April 2025|
A.Muhammad Birnin Magaji, Shu’aibu A. Jangebe
Zamfara Radio Gusau. ZACAS, Gusau.
Tsakure
Wannan bincike ya yi tsokaci ne a kan hikimar roƙo a cikin wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, binciken ya kawo ma’anar roƙo da rabe- rabensa, da kuma hikimar saƙala roƙo a cikin waƙoƙin Kassu, domin isar da saƙo. Haka kuma, binciken ya dubi hanyoyin gudanar da bincike, da ra’in bincike da kuma bayani a kan sakamakon abin da binciken ya gano. Sai kammalawa daga ƙarshe.