DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.60 |Issue 1 | April 2025|
Maryam Tukur Ibrahim
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari, Sokoto
Tsakure
Wannan maƙala mai taken Kalaman Gaskiya da na Ƙirƙira a Bakin Kassu Zurmi Nazari Daga wasu Waƙoƙinsa: Ta Kalli irin yadda Kassu ke fitowa da mazaunin gaskiya da yadda yake furta wasu kalamai na ƙirƙira a cikin waƙoƙinsa domin ya kwarzanta waɗanda yake yi wa waƙa. Gaskiya da ƙirƙira kuma, al’amura ne masu buƙatar bayanin gaske a rayuwar Ɗan’Adam ta yau da kullum, Don haka maƙalar ta kawo ma’anar waƙa da gaskiya da ƙirƙira. An kuma kawo misalai na wasu waƙoƙin Kassu Zurmi inda yake furta wasu kalamai da suka danganci gaskiya da kuma waɗanda suka danganci ƙirƙira domin yin yabo ko zuga ga gwanayensa. Don kwarzanta su su yi suna, Har ila yau maƙalar ta kalli yadda mutane suke kallon maganar ƙirƙira da maganar gaskiya a rayuwar yau da kullum. Da yake mafi yawan mawaƙan, Hausa da masu saurarensu Musulmi ne kuma addininsu ya nuna masu ƙa’idojin rayuwa ta duniya da ta lahira da abubuwan da ke iya wanzuwa da waɗanda ba su iya wanzuwa, kuma babu mai iya wanzar da su in ba Allah (S.W.A) ba. An kammala da bayar da shawarwari an kuma kawo manazarta domin kafa hujja