DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.49 |Issue 1 | April 2025|
Abdullahi Yunusa
Tsakure
Wannan maƙalar ta yi tsokaci ne game da rukunin kalmomi na Bayanau da ma’anarsa da yanayin yadda akan yi amfani da su a cikin jumlolin Hausa. Mawaƙi Kassu Zurmi yana daga cikin mawaƙan Hausa, waɗanda sukan yi amfani da irin waɗannan kalmomi na Bayanau acikin waƙoƙinsa. Maƙalar ta nazarci irin kalmomin Bayanau da yakan yi amfani da su, waɗanda hakan shi ya ƙara fito da zurfin fahimtarsa da naƙaltarsa ga harshen Hausa. Saurare da kuma nazartar waƙoƙinsa su ne hanyoyin da aka yi amfani da su a yayin gudanar da wannan maƙalar.