DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.16 |Issue 1 | April 2025|
Ibrahim Dalha
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Tsakure
Duk da cewar waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi sun fi mayar da hankali a kan rukunin maza (‘yan tauri); hakan bai hana a iya ƙyllaro hoton wasu mutane a cikinsu ba. Wannan takarda ta dubi rukunin masu fama da nakasar kisan-raɓa a waƙoƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa ‘yan taurinsa. Nazarin ya mayar da hankali ga waƙar Shayi ɗan gidan Labbo a matsayin karan bara. Domin yi wa binciken adalci, an waiwayi ayyukan magabata wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba. Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance. Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe (karin magana) da ke cewa: “Maƙwabcin mai kanwa ba ya rasa ɗan ɓarɓashi” a matsayin hanyar ɗora aiki. Wasu daga cikin sakamakon da nazarin ya gano sun haɗa da: Nakasar kisan-raɓa ɗaya ce daga cikin larurorin da suke addabar wasu mutane. Har wa yau, kisan–raɓa nakasa ce da ta shafi mutuwar zuciya, don haka ba a ganin ta ƙuru-ƙuru da ido, sai dai ayyukan wanda ta kama su nuna. Bugu da ƙari, Kisan-raɓa nakasa ce da takan riski wasu a dalilin sakaci, wasu kuma ƙaddara ce ta riga fata. Daga cikin shawarwarin da takardar ta gano sun haɗa da, akwai buƙatar al’umma su sanya wa kansu kishin kai, ta yadda kowa zai tashi ya nemi na kansa kamar yadda magabatanmu suka gudanar da rayuwarsu. Haka kuma, sanya yara a tafarkin jin daɗi, wani abu ne da zai ci gaba da haifar da wannan larura. Domin ko ba komai, idan muka tuna magabata, masu larurar makanta da gurgunta duka suna tashi tsaye su yi sana’a domin samar wa kansu mafita.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Halaye da Kisan-raɓa da kuma ‘Yan Tauri