DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.7 |Issue 1 | April 2025|
1Bashar Abdullahi, 1Mustafa Umar, 1Saifullahi Ahmad Madawaki
1Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Jihar Sakkwato
Tsakure
Wannan takarda tana da ƙudurin dubin lokutan gargajiyar Hausawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi. Nazarin ya mayar da hankali ga fito da yanaye-yanayen lokutan da suka yi amo a waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi. Binciken ya waiwayi ayyukan magabata waɗanda suke da alaƙa da nazarin. Wasu daga cikin hanyoyin tattara bayanan da aka yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi da gudanar da hira ko tattaunawa da waɗanda suke da masaniya game da nazarin da aka gudanar, sai kuma karance-karance. Maƙalar ta yi amfani da tunanin Bahaushe da ke cewa: “Akwai ruwa a ƙasa, sai ga wanda bai tona ba” a matsayin hanyar ɗora aiki. Wasu daga cikin sakamakon da aka gano sun haɗa da: Hausawa suna da tsarin lokacinsu tun kafin su cuɗanya da wasu al’ummu. Waƙoƙin Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi suna ƙunshe da al’adun Hausawa waɗanda suka shafi zamantakewarsu da kuma yanayin yadda suke amfani da lokatai. Haka kuma, Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi ya yi amfani da lokatan damina da na rani a waƙoƙinsa domin nuna matsayinsu da kuma tasirinsu a rayuwar Hausawa.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Lokuta da Gargajiya da kuma Baki.