DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.24  |Issue 1 | April 2025|

Sakina Adamu Ahmad    

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya., Jami’ar Jihar Sokoto

Tsakure   

Wannan maƙala tana magana a kan matsayi da alaƙar jinsin mata a sana’ar tauri da ‘yan tauri, tare da wasu taurari da suka fito a waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi. Bincike ya fahimci cewa, a al’ummar Hausawa duk irin ɗauki-ba-daɗin da ake na rayuwa ba ya kammala idan ba mata a ciki, domin su ne abokan tafiyar maza.. Waƙoƙin makaɗa Kassu, sun keɓanta kan waƙoƙin maza a ɓangaren tauri da farauta da sata. Waɗannan al'adu ne na  jarumtaka da suka ba da  }arfi ga jinsin  ga maza saboda yanayin halitta da kuma al'adun al’ummar Hausawa, amma wannan bai hana mawaƙin ya ambato wasu ɗaiɗaikun mata abokan tafiya da suke da kusanci da tauri da ‘yan tauri da irin rawar da suka taka a cikin lamarin tauri. Manufar binciken shi ne fito da matsayin waɗannan matan da irin gudummuwarsu ga abokan zamansu. Ma}alar ta yi duba kai-tsaye ga waɗannan matan domin fito da gudummuwarsu a cikin tafiya da kuma irin dangantaka da alaƙar da suke da ita da wasu fitattun ‘yan tauri. Binciken ya tattaro bayanai ta fuska biyu; wato ta bibiyar waƙoƙin mawaƙin domin zaƙulo baitukan da ma waƙoƙin da aka ambacin matan. Akwai yin hira da masana da waɗanda ke da dangantaka da matan don jin wani bayani da ya shafi rayuwarsu da inda suka haɗa da yan tauri. Sakamakon wannan bincike ya yi hasashen cewa mata sun samu matsayi a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, matsayi mai kusanci da sana’ar tauri da ‘yan-tauri daidai jinsinsu da iyawa da ƙwarewarsu a rayuwa.