DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.25 |Issue 1 | April 2025|
Shu’aibu A. Jangebe, Y. Halilu Anka, Saifullahi A. Madawaki ZACAS, Gusau
Tsakure ]
Wannan bincike ya yi tsokaci ne a kan karin magana da kirari a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi. Binciken zai kawo ma’anar karin magana da kirari da muhimmancin da kuma tarihin mawaƙin a taƙaice sai kuma yadda mawaƙin ke tsalma karin magana da kirari a cikin waƙoƙinsa. Farfajiyar bincikenmu kuma shi ne, wannan bincike kuma zai taƙaita ne kawai a wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi. Hanyoyin gudanar da wannan bincike shi ne, an yi amfani da wasu wallafaffin littattafai da Muƙalu da tattaunawa da wasu mutane da suka san waƙoƙinsa, tare da sauraron waƙoƙinsa da ke cikin “C.D” da kuma kasusuwa. Sai ra’in bincike. Wannan bincike an ɗora shi ne a kan ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau, 2003, 2008, da 2014. Sai kuma sakamakon bincike da kuma naɗewa, da za a yi duk a cikin wannan binciken.