DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.28 |Issue 1 | April 2025|
Nasara Bello Dogon Daji
Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar, Sakkwato
Tsakure
Mawaƙa na da hanyoyi iri-iri fa suke bi wajen aiwatar da waƙoƙinsu da kuma amfani da salailai nau’i-nau’i domin sanya armashi. Wannan maƙala mai suna, “Mawaƙi Ɗaya Muryoyi Goma: Nazarin Kwaikwayon Muryoyi a Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” maƙala ce da ta yi nazarin ɗaya daga cikin hikimomin da waƙoƙin Kassu Zurmi suka ƙunsa wato kwaikwayon muryoyi daban-daban na mutane da ma wasu sauran halittu. Maƙalar ta yi amfani da waƙoƙi kamar waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi Ɗangidan Labbo da waƙar Muhammadu Fatake na Dare haka kuma ana iya lalubo misalai daga wasu waƙoƙi masu salo makamancin na Kassu Zurmi. Manufar wannan maƙala ita ce a dubi irin hikimar Kassu wajen kwaikwayo a cikin waƙarsa, sannan a dubi shi kansa kwaikwayon yadda ya rarraba da kuma yadda ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa. Bincike maƙala dai ta jingina ne falsafar waƙe Magana ta Hausawa da ke cewa « Kai kaɗai gayya” da ma dai Kassu Zurmi ba karɓi ake masa ba, saboda haka duk hira da tattaunawar da ka ji cikin waƙoƙinsa duk shi kaɗai ne ke hidimar sa. Abin da binciken wannan maƙala ya gano shi Kassu Zurmi ya yi amfani da dabarar mawaƙa ta amfani dabarar kwaikwayon mutane har ma da amfani da adon harshe da wasu masana suka kira jinsarwa wasu kuma suka kira shi jinsantarwa. Mawaƙin ya jinsantar da tsuntsaye da karkuna.