DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.45     |Issue 1 | April 2025|

Yunusa Ibrahim Adamu 

Farida Muhhamad Amin

 Cibiyar Nazarin Hausa,  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. 

Department of Hausa,  Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies Kano.

Tsakure   

Manufar wannan takarda ita ce, ta fayyace irin gudummuwar da Kassu Zurmi ya bayar ta fuskar waƙoƙin Farauta a ƙasar Hausa. An yi amfani da nau’in sharhantaccen bincike bi bayani (descriptive }ualitative method) wajen gina wannan takarda. Haka kuma, an ɗora wannan bincike a kan ra’in waƙar baka Bahaushiya (WBB ) Wanda (Gusau, 2003, 2008, 2014) ya assasa. Musamman ɓangaren da ya yi magana a kan Turke da hanyoyin binciko manya da ƙananan turaku da tubalai a waƙar baka ta Hausa. Da kuma salo da sarrafa harshe. A wajen tattaro bayanan wannan bincike, an yi amfani da hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da; tattaunawa da masu sha’awar waƙoƙin baka na Hausa, musamman waƙoƙin maza na farauta da dambe da tauri da sauransu. An yi bitar matanin waƙoƙi biyu na farauta da Kassu Zurmi ya aiwatar domin a samu damar ƙalailaice turke da tubala a cikinsu. Binciken ya gano cewa Kassu Zurmi masani ne a kan abin da ya shafi al’adun ƙasar Hausa musamman ɓangaren amfani da magungunangargajiya domin neman tsari ko kariya daga abokan gaba da namun daji da aljanu ko iskoki. A wasu lokutan yakan yi amfani da dabarun jawo hankalin masu sauraron waƙoƙinsa wajen yin karin magana da zambo da habaici domin kushe abokan adawa a farauta. A ƙarshe binciken ya gano cewa, Kassu Zurmi yakan yi amfani da salon kamantawa da kwatantawa da siffantawa da jinsintarwa da mutuntarwa da dabbantarwa da kambamawa da alamtarwa duk a cikin waƙoƙinsa na farauta.  Haka kuma, binciken ya lura da wasu tubalai da yake amfani da su. Irin waɗannan tubalai sun haɗa da na yabo da zuga ta hanyar bayyana jarumtar mafarauta da irin haɗarurrukan da suke cin karo da su a daji.   Fitulun Kalmomi: Waƙar baka, Gudummuwa, Waƙoƙƙin maza, Farauta, jarumta.