DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.26   |Issue 1 | April 2025|


Yakubu Aliyu Gobir  

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto

Tsakure 

Manufar wannan maƙalar shi ne fito da gudummuwar waƙoƙin Kassu Zurmi wajen samar da tsaro. Maza su ke samar da tsaro kuma su ke wargaza shi. An saurari waƙoƙin Kassu Zurmi da aka taskace cikin wasu ayyuka da kuma tattunawa da masana da manazarta, domin samo bakin zaren matsalar tsaro, kamar yadda Kassu Zurmi ya fito da su. Aikin ya gano cewa, tsaro ba ya samuwa a cikin al’umma har sai mahukunta sun yi aikinsu, su kuma jama’a sun taimaka musu. Barin jama’a suna ɗaukar mataki/doka a hannunsu ba shi ne mafita ba.