DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.13    |Issue 1 | April 2025|

Haruna Umar Maikwari, Muhammad Shu’aibu Abubakar   Department of Hausa Language, Federal College of Education (Technical) Gusau

Tsakure Tsakure 

Al’adun kyautata zamantakewa, al’adu ne masu ɗimbin yawa da har yau ba a ƙayyade su ba, da ma dai alada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Don haka dukkan tsarin da aladar mutane ta yarda da shi, bin sa kyautatawa ne kuma kauce masa na hardasa rashin kyautatawa. Makaɗa Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne, duk da cewa a baya ya yi wa ɓarayi waƙa. Wannan maƙalar tana da manufar fito da wasu aladun Hausawa na kyautata zamantakewa a cikin wasu waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi. Haka kuma za a nazarci al’adun tare da fayyace muhimmancin riƙo da su. Za a yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu domin cimma burin wannan maƙala. Hanyar ɗora aiki da aka yi amfani da ita kuwa, ita ce ta amfani da karin maganar nan ta “Da tsohuwar zuma ake magani”. Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa akwai nason wasu aladun kyautata zamantakewa a cikin waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi duk kuwa da cewa wasu waƙoƙin ya yi su ne ga masu iƙirarin tsiya kamar yadda ya kira wasu daga cikinsu (‘yan tauri).