DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.6 |Issue 1 | April 2025|
Badamasi Altine Kasarawa1, Habibu Lawali Kaura2, Sadiya Abdullahi Gusau1
Sashen Hausa Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Sakkwato.
Sashen Hausa Kwalejin Ilimi da Ƙere-Ƙere ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau Zamfara
Tsakure
Wannan maƙala ta bibiyi wasu waƙoƙin Abubakar Kassu Zurmi, domin fito da nau’o’in abincin Hausawa na gargajiya da suke ƙunshe a ciki. Haka kuma, maƙalar ta kafa hujja da waɗansu ɗiyan waƙoƙi da suke tabbatar da cewa, zane na mai shi ne, kowa ya laga aro ya yi. Watau kenan, duk nau’o’in abincin da Kassu Zurmi ya ambata a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka kawo a cikin wannan maƙala, to abincin Hausawa ne. Sai dai dalilin cuɗanya da waɗansu baƙi al’umma, ya sa a yanzu an samu ƙarin nau’ukan abinci da Hausawa suke amfani da shi wanɗanda ba na gargajiya ba ne. Daga cikin abubuwan da wannan maƙala ta gano su ne, dalilin cuɗanya da baƙin al’umma, Hausawa wasu sun fara raja’a ga sababbin nau’ukan abincin zamani saɓanin na gargajiya. Ƙananan yara masu tasowa kuma, ba su san sunayen nau’ukan abincin Hausawa na gargajiya ba.