DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.62 |Issue 1 | April 2025|
Sirajo Mukhtar
Sashen Hausa, Jami’ar Ilimi Ta Tarayya, Zaria
Tsakure
Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo irin fasahar da hikimar da Allah ya yi wa makaɗa Kassu Zurmi a fagen waƙa, tare da bayyana irin yadda yake amfani da nau’o’in Adon harshe daban-daban waɗanda ke ƙarawa waƙarsa armashi, kwalliya da karɓuwa ga masu sauraronsa. Makaɗa Kassu Zurmi mashahurin mawaƙi ne na zamaninsa. An yi hira da wasu masu sauraron waƙarsa, kuma an saurari waɗansu daga cikin waƙoƙin nasa, sannan an yi bitar waƙoƙinsa wadda shi ya sanya aka samo waɗansu muhimman bayanai wadda za su taimaka ma takardan da za a gabatar. Inda aka gano cewar yana amfani da nau’o’in adon harshe daban-daban irin su kamantawa, jinsintarwa, habaici, alamtarwa ko kinaya, abuntarwa da sauransu. A dalilin amfani da waɗannan nau’o’in adon harshen sun saka waƙoƙinsa sun samu karɓuwa da kuma rashin ƙosawa ga masu sauraronsu da kuma manazarta. A wannan takarda an yi nazarin adon harshe ne a wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi. Waɗanda suka haɗa da waƙar Daɗi na Amadu da kuma waƙar ‘yan jabanda.