DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.63 |Issue 1 | April 2025|
Tukur Mode Sifawa
Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sokoto
Tsakure
Wannan takarda mai taken “Nazarin Aikatau a Cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi” ta yi sharhin aikatau dangane da abin da ya shafi giredi, musamman dangane da Hausar Yamma. Harshen Hausa kamar wasu harsunan duniya, shi ma yana ɗauke da ajin aikatau a cikin sa. Manufar wannan takarda ita ce fito da kuma yin nazarin wasu kalmomin aikatau da makaɗa Kassu Zumi ya yi amfani da su a cikin wasu daga cikin waƙoƙinsa, domin aza su bisa ga sikeli a ga wane giredi za su iya hawa da wanda ba za su iya hawa ba. An yi amfani da hanyar sauraren waƙoƙin ne kamar sau biyu ko uku ko ma fiye da haka a wani lokaci domin a fitar da nau’o’in aikatau da ake nema tare da karanta littattafan da aka rubuta waƙoƙin. An yi amfani da hanyar bayanin aikatau da F.W Parsons ya assasa a shekarar 1960, wanda Amfani ya faɗaɗa a 1995 da 2005. Wannan takarda ta gano kusan dukkan aikatau sha-rinjaye da aka yi amfani da su masu gaɓa biyu ko uku suna iya ɗaukar mafi yawa giredin ko darajojin nan guda bakwai, amma za a yi amfani da aikatau mai gaɓa bibbiyu, musamman wanda ya shafi giredi na biyar domin ganin yadda suka bayyana a Hausar Yamma.