DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.34    |Issue 1 | April 2025|

Bilkisu Yusuf Ali 

Sashen Koyar da Harsunan Afrika (Hausa Unit), Jami’ar Al-Ƙalam, Katsina

Tsakure  

Manufar wannan takarda ita ce yin ninƙaya cikin waƙoƙin Abubakar Kassu domin fito da wasu zantuka waɗanda suka ci karo da addini ko al’ada kamar yadda suka wanzu a waƙoƙin makaɗin. Daga cikin ire-iren waɗannan zantuka akwai zage-zage da ingiza mai kantu ruwa da kisan kai da sauransu. Ra’in da aka ɗora wannan nazari shi ne “Ra’in Fanɗararrun Jigogi”. Daga cikin hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan nazari sun haɗa da; sauraron wasu waƙoƙin marigayi Abubakar Kassu Zurmi don fito da waɗannan turaku.Kazalika, an leƙa cikin wasu ayyukan magabata masu alaƙa da nazarin don samunbayanai da za su taimaka wajen nasarar binciken. Daga cikin sakamakon binciken an fahmci makaɗa Abubakar Kassu yana amfani da waɗannan turaku ga mutanen da suke aiwatar da wasu ayyuka na jaruntaka domin kambama su. Haka kuma, amfani da waɗannan zantuka kan saka karsashi da nisahaɗi ga jarumansa. Bugu da ƙari, an gano wasu zantukan sun ci karo da karantarwar addinin Musulunci.