DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.52     |Issue 1 | April 2025|

Bello Usman Liman 

Raihanatu Umar Garba 

Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar Sakkwato Ummaru Ali Shinkafi Polytechnic, Sokoto State

Tsakure

Mawaƙan Hausa mutane ne da Allah ya ba su hikima da baiwa ta wani muhimmin runbun adana tarihi da bunƙasa harshe da al’adu da adabin Hausa.  Hakan ya sa ake samun abubuwa da yawa masu muhimmanci a waƙoƙinsu. Manufar wannan maƙala ita ce nazarin jumlolin tambaya a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi. Kasancewar duk maganar da ɗan adam ke furtawa sautuka ne ake harhaɗawa, a samu gaɓa, a haɗa gaɓoɓin a samar da kalma, a haɗa kalmomin a samar da jumloli a harshe. Masana nazari harshe sun rarraba jumlolin Hausa ko dai ta fuskar tsarin jumlolin ko kuma ta fuskar aikinsu, a wannan takarda za a dubi  nau’o’in jumloli ta fuskar aikinsu, amma wannan takarda za ta mayar da hankali kan jumlolin tambaya da Kassu ya yi  amfani  da su a cikin wasu waƙoƙinsa da maƙasudin yin tambayar, kamar tambaya ta sigar roƙo ko tambaya ta sigar ƙalubalanta da ta gwarzantawa da kuma ta fuskar kiranye. Wannan takarda ta gano cewa a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi akwai ɗinbin jumlolin tambaya ko masu sigar tambaya cikinsu. Don haka ne wannan takardar ta taskace wasu daga ciki, kuma ta yi cikakken sharhi a kan su.