DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.36 |Issue 1 | April 2025|
Fauziyya Muhammad Hassan
Tsakure
Takardar ta yi bayani a game da Nazarin Jinsintarwa ne a waƙar baka. Jinsintarwa na nufin yadda mawaƙa suke bin wasu dabarun kwatance daban-daan wajen kambama ko kururuta ko zuga ko kushe kansu ko iyayen gidansu ko kuma wasu makusantansu. Mawaƙan maza suna amfani da salon jinsintarwa wajen fito da martaban mafarauta ko ‘yan dambe ko ɓarayi da wasu iyayen gidansu, kamar yadda aka sami hakan a wasu ɗiyan waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi wanda hakan ya haifar masa da wani tasiri da shura da kuma tabbatar da irin sunan da ya yi a idon duniya. Takardar ta bi hanyoyin tattara bayanai kamar shiga ɗakunan karatu inda aka dubi ayyukan magabata da suke da alaƙa da wannan batu. An kuma saurari faya-fayan waƙoƙin Kassu Zurmi tun daga na kaset-kaset waɗanda ake saurara a ji da kuma faya-fayan (CD) waɗanda ake saurara a ji kuma a gani. Binciken ya tabbatar da cewa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi ya bayar da gudummuwa musamman wajen kare martaban harshen Hausa da kuma adana wa harshen wasu hikimomi da tarin kalmomi da baiwar da Allah ya yi masa.