DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.33    |Issue 1 | April 2025|

Anas Sa’idu Muhammad, Nuhu Abbdullahi Jibril, Binta Ibrahim Jibrin   

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano Ɗalibin Ph.D Hausa (Culture) Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano

Tsakure 

Manufar wannan takarda [1] ita ce a aiwatar da nazari kan wasu waƙoƙin Kassu Zurmi yadda yake amfani da tubalin koɗawa da washi wajen gina gundarin saƙo a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. An ɗora mizanin tarken wannan takarda ne bisa ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB), wanda Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya assasa (2003, 2008, 2014, 2022, 2024). Sannan kuma, a wannan takarda za a yi amfani da nau’in bincike na bi-bayanin sharhantaka (Descriptive }ualitative Research) wajen fiɗar bayanan bincike. Haka kuma za a yi amfani da tsarin samfuri bi-maƙasudi (Purposive Sampling) wajen zaɓe da juyar waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda suka ɗarsu da tubalin koɗawa da na washi. Kamar yadda Gusau (2022). Saboda haka, wannan takardar za ta yi ƙoƙari wajen tantancewa tare da fayyace yadda Kassu Zurmi ke amfani wajen fito da tunaninsa da gaibiyyarsa cikin hikima da zalaƙar harshe wajen amfani da ƙananan saƙonnin ya koɗa ko kuma ya yi washi ga ɓarayi ko mafarauta ko kuma ‘yantauri a zubin ɗiyan waƙoƙinsa. Za a iya cewa, koɗawa da washi naɗaya daga cikin ginshiƙan ƙananan tubalan da KassuZurmi ke amfani da su wajen sauya tunanin masu sauraron waƙoƙinsa.Domin a mafi yawancin zubin waƙoƙinsa, Kassu Zurmi gwani ne musamman wajen ƙagowa da sauwarawa da kimantawa tare da kuma kwaikwayar haliyya da bajinta da kuma ɗabi’un mafarauta ko `yantauri ko kuma ɓarayi da dai sauransu a zubin ɗiyan waƙoƙinsa.Yana amfani da tubalan koɗawa da na washi  ne ya fayyace wani abin arziki, ko bajinta ko waibuwa ko hazaƙa ko wata ɗaukaka da Allah mai girma ya ba wanda yake yi wa waƙa a fagen fama ko na gwajin-sa’a ko na daga ko na yaƙi da dai sauransu. 


Keɓaɓɓun Kalmomi:Ɓarayi; Koɗawa;Mafarauta; Washi; `Yantauri