DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.61 |Issue 1 | April 2025|
Mukhtar Ahmad
Al-Ƙalam University, Katsina Faculty of Humanities Department of African Languages
Tsakure
Wannan maƙala tana bincike ne a kan ma’anar wasu kalaman da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a waƙoƙinsa domin ya fito da ma’anar abin da yake magana a kan sa. A wannan nazari an yi amfani da ra’in aiwatarwa. Kuma an tattara bayanan wannan maƙala daga waƙoƙin Kassu Zurmi da littattafan ilimin ma’ana da kuma ƙamusoshin Hausa. A cikin wannan maƙala an kawo matsayin kalma ko jimla a ilimin ma’ana tare da bayanin ma’anarta. A ƙarshen wannan binciken an gano matsayi da ma’anonin kalamai da yawa na Kassu Zurmi a waƙoƙinsa daban-daban. Kamar ma’ana ‘Ɗa’ tana iya ɗaukar ma’anoni irin wanda aka haifa namiji, wanda ba bawa ba, mutum mai mutunci da sauransu. Wannan bincike gudummuwa ce ga koyo da koyarwa a harshen Hausa.