DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.8    |Issue 1 | April 2025|

Buhari Lawali, Lubabatu Ibrahim, Nuruddeen Abubakar

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato

Tsakure

Wannan maƙala ta yi nazarin neman auren Hausawa a cikin waƙar Makaɗa Abubakar Kassu Zurni ta Shayi ɗan gidan Labbo. Manufar  wannan maƙala ita ce, fito da wasu aladun neman aure,  da kuma nuna irin hanyoyin da Hausawa suke bi domin tantance wanda za a aura, kamar yadda Kassu Zurmi ya bayyana a cikin waƙar Shayi ɗan gidan Labbo. An bi hanyar nazarin rubuce-rubucen ilimi da sauraren waƙar Makaɗa Abubakar Kassu ta Shayi ɗan gida Labbo domin fito da yadda ake neman aure a al’adar Bahaushe. Sakamakon binciken ya gano cewa, Bahaushe yana gudanar da bincike kafin ya yarda ya aurar da ɗiyarsa. Haka kuma an gano Bahaushe yana ba ’ya’yansa mata damar zaɓen wanda suke so su aura.