DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.30   |Issue 1 | April 2025|

 Adamu Lawal 

Sashen Hausa Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna, Gidan Waya, Kafanchan. Kaduna, Nijeriya.


Tsakure 

An lura cewa manufar wannan muƙala ita ce nazarin nau’o’in zuga daga wasu waƙoƙi da wannan shahararren makaɗi ya tsara, domin a gano sigoginsu da tasirinsu a waƙoƙinsa. A ƙarshe muƙalar ta ci nasarar gano cewa waƙoƙin makaɗa Abubakar Kassu Zurmi ɗamfare suke da nau’o’in zuga ta sigogi da dama. Harwayau waƙoƙin sun ƙunshi nau’o’in zuga kumburau domin hura gwani, da zuga kaiyau, domin kare gwani daga hawan ƙawara na abokan hamayya, sai kuma zuga ingizau da yake tunkuɗau gwaninsa ya aikata abin da ake so koɗa babu niyya. Ƙwarewarsa a wannan salo da sauran salailai da yake sarrafawa a waƙoƙinsa, ya sanya ya yi fice a ƙasar Hausa ake gayyatarsa wuri-wuri domin nishaɗantar da masu saurare, musamman gidajen rediyo a ƙasar nan.