DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.43     |Issue 1 | April 2025|

Nasir Abdullahi Usman,   

Bashir Aliyu Tsafe

 Federal University Of Education, Zariya, Jihar Kaduna Nigeriya 

Federal College of Education Ƙtechƙ, Gusau, Jihar, Zamfara 

Tsakure 

An lura cewa manufar wannan takarda shi ne yin nazarin zuga daga cikin wasu waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurma da kuma irin tasirin da zugan yake da shi a waƙar. Inda ƙarshen takardar ta gano cewa waƙoƙin Alhaji Abubakar Kassu Zurmi kusan gaba ɗaya ɗauke suke da salon zuga ta hanyoyi masu yawa. An ɗora wannan bincike kan Ra’in Awon Baka (Oral Formulaic Theory) wanda Philips Viscey (1767-1834) mutumin ƙasar Sabiya ya ƙirƙira kuma ya yaɗa shi har zuwa wasu sassa na Turai da Amurka. A ƙarshen wannan takarda  an gano cewa mafi yawan waƙoƙin Kassu Zurmi cike suke da salon zuga a cikinsu.