DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.21 |Issue 1 | April 2025|
Nazir Ibrahim Abbas, Aminu Umar Alkammawa Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto Department of History and International Studies, Faculty of Arts Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Tsakure Suna linzami wannan zancen Hausawa haka yake ko a cikin fahimtar masana ilimin kimiyyar harshe domin kuwa da sunan mutum ko abu ake gane shi ko bambanta shi da wani. Masana harshe sun aminta cewa kalmomin sunaye a kowane harshe suna da ma’ana kuma akwai ra’in da ake nazarin sunaye ta la’akari da asalinsu ko tarihinsu ko kuma yadda suka bayyana tare da sauye-sauyen da suke samu. Wannan maƙala mai taken: Nazarin Sunaye a cikin Wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi ta yi fito da wasu sunayen da marigayi Alhaji Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin wasu waƙokinsa guda goma sha ɗaya da aka yi nazari. Manufar maƙalar ita ce nazarin waɗannan sunayen a bisa faifan nazarin sunaye a fagen ilimin kimiyyar harshe (onomastics) wanda yake nazarin kalmomin sunaye da kuma rarraba su ta la’akari da asali da tarihi da kuma yadda aka samar da su. An yi amfani da wannan ra’in ne wajen nazarin rukunin sunaye na wurare da ɗaiɗaikun mutanen da Kassu Zurmi ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin. Binciken ya yi amfani da dabarun bincike na sauraren waƙoƙin da kuma karanta wasu matanin waƙoƙin Kassu Zurmi da aka rubuta wajen tsamo irin waɗannan sunayen da kuma rarraba su a cikin rukunan da aka same su kamar yadda wannan ra’in ya tanada. Bimciken ya taƙaita ne kawai ga nazarin waƙoƙi goma sa ɗaya (11) na Kassu Zurmi da suka ƙunshi waƙoƙin tauri da waƙoƙin farauta da waƙoƙin ɓarayi inda aka fito da adadin sunayen guda ɗari biyu da bakwai (207) da suka haɗa da sunayen wurare (garuruwa da ƙauyuka) da sunayen ɗaiɗakun mutane da aka rarraba a cikin rukunin; sunayen yanka da sunayen laƙabin dangantaka da sunayen gargajiya da sunayen sarauta da kuma sunayen jaruntaka ko kirari. Daga waɗannan sunayen da aka samu binciken ya tabbatar muna da fahimtar mafi yawan duniyar da marigayi Kassu Zurmi ya rayu a cikinta da kuma inda ya yi waƙoƙinsa a lokacin rayuwarsa da mutanen da ya yi wa waƙoƙin musamman kasancewar wasu sunayen da an ji su ko da ba a cikin waƙoƙinsa ba ne wanda ya saba sauraren waƙoƙin zai iya tunawa da lalle wannan suna fitacce ne a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi.