DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.40    |Issue 1 | April 2025|

Muhammad Isa Usman 

Ɗalibi a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.  

Tsakure 

Manufar wannan takarda ita ce yin nazarin dabarar takidi a cikin ɗiyan waƙoƙin Kassu Zurmi ta duban takidi na saɗara ɗaya da farkon ɗan waƙa da tsakiyar ɗan waƙa da ƙarshen ɗan waƙa da kuma maimaita ɗan waƙa guda. A wannan takarda an yi amfani da Mazahabar Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) ta Gusau  a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a kansa. Haka kuma, an yi amfani da dabarar bincike bi-bayani wajen yin sharhi da bayanin ɗiyan waƙoƙin Kassu Zurmi masu ɗauke da dabarar takidi. Binciken ya gano cewa, Kassu Zurmi ba ya yin takidi na karɓeɓeniya da Bayayyeniya a cikin waƙoƙin a sanadiyar kasancewarsa makaɗin kaɗaita.  

Fitilun Kalmomi: Takidi, Ɗiya, Kassu Zurmi, Waƙa