DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.51 |Issue 1 | April 2025|
Bello Usman Liman
Usman Ibrahim Ka’oje
Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts, Sokoto State University, Sokoto
Adamu Augie College of Education, Argungu
Tsakure
Wannan takardar za ta mayar da hankali ne kan ilimin ma’anar kalmomi waɗannda suka shafi yalwar ma’ana a cikin waƙoƙi biyu na Alhaji Abubakar Kassu Zurmi, waƙar Nomau na Magarya da waƙar Shayi ɗan gidan Labbo. Waƙa wata baiwar fasaha ce da Allah maɗaukakin sarki ya baiwa wasu mutane ta fasaha ta yadda suke amfani da kalmomi su sarrafa su yadda suka ga dama a cikin harshe. Kassu Zurmi na cikin irin waɗannan mutane da ke amfani da wannan hikima a cikin waƙoƙinsa. Wannan ya ja hankalin wannan takardar har ta dubi kalmomi masu yalwar ma’ana a cikin masu waƙoƙinsa, kuma tayi sharhi akansu ta fuskar ilimin ma’ana, tare da cikakken nazari ta wannan fuskar. wannan takarda ta yi amfani da hanyoyi guda biyu kamar haka karanta waƙokin a rubuce da kuma saurarensu da kunne. Da ga ƙarshe wannan takardar ta gano akwai kalmomi masu yalwar ma’ana masu tarin yawa a cikin waɗannan waƙoƙin da wannan takarda tayi nazari a cikinsu