DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.20   |Issue 1 | April 2025|

Musa Fadama Gummi, Abdullahi Sarkin Gulbi   

Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodoyo, Sokoto

Tsakure 

Wannan muƙala ta bibiyi wasu waƙoƙi na makaɗa Kassu Zurmi domin zaƙulo wasu kyawawan aladun Hausawa da suke ƙunshe a cikinsu. Muƙalar ta tattaro waƙoƙi da dama na Kassu, na sata da na tauri. An saurari waƙoƙin gwargwado domin ganin ko za a iya tsintuwar dami a kala. Sakamakon wannan bincike ya gano cewa duk da Bahaushe yana yi wa waƙoƙin sata da tauri wani kallo na abubuwan da suka bijire wa addini, ana iya samun kyawawan  aladun Hausawa da ma wasu tubula a cikin waƙoƙin waɗanda ke gina tarbiyya da halayya ta gari, kamar amana da kirki da gaskiya da taka tsan-tsan da ƙanaa da dai sauransu. Wannan ne ya sa muƙalar take ganin cewa sauraron waɗannan waƙoƙi na iya zama wata tudun dafawa na cusa kyawawan halaye da dabarun zaman duniya ga masu sauraron su. 

Fitattun Kalmoni:  Masaƙa, Tsattsafi, Al’adu, Waƙoƙi