DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.50     |Issue 1 | April 2025|

Abdullahi Yunusa 

Tsakure

Wannan maƙalar za ta yi tsokaci ne game da rukunin nau’o’in kalmomi na Tsigalau da ma’anarsa da yanayin yadda akan yi amfani da su a cikin jumlolin Hausa. Mawaƙi Kassu Zurmi yana daga cikin mawaƙan Hausa, waɗanda sukan yi amfani da irin waɗannan kalmomi na Tsigalau a cikin waƙoƙinsa. Maƙalar za ta nazarci irin kalmomin Tsigalau da irin yadda yakan yi amfani da su, waɗanda hakan shi ya ƙara fito da zurfin fahimtarsa da naƙaltarsa ga harshen Hausa. Saurare da kuma nazartar waƙoƙinsa su ne hanyoyin da aka yi amfani da su a yayin gudanar da wannan maƙalar.