DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.44     |Issue 1 | April 2025|

Muhammad Sani Umar Kulumbu 

Abdullahi Haruna Imam 

School of Languages, A.D. R ufa’i College of Education, Legal and General Studies, Misau, Bauchi State. 

Faculty of Arts and Education, Department of Languages and Linguistics , Yobe State University, Damaturu

Tsakure  

Wannan takarda ta yi nazarin salon da mawaƙi Kassu Zurmi yake amfani da shi ne a waƙarasa wajen bayar da labarin baka a cikin waƙoƙin da yake yi. Manufar takardar ne ta nazarci irin wannan salon na bayar da labari a waƙar da aka yi ta Sarkin Gabas na Gusau. A cikin waƙar Kassu ya faɗi yadda ta kaya a tafiyarsu Daba Gusau, musammam abin da ya faru a garin Bunguɗu. An yi ƙoƙarin fito da irin hikimar da Kassu yake bi wajen jawo hankalin masu sauraron waƙarsa ta hanyar bayar da labarin baka. An ɗora wannan aikin bisa ra’in Nazarin Salon Bayar da Labari a Waƙar Baka ta makarantar Gusau (1999). Nazarin ya fito da salon bayar da labarin baka cikin rauji da kiɗi. Gusau (2008) yana mai cewa mawaƙa da makaɗan baka kan aiwatar da waƙoƙi kan wasu abubuwa da suka faru a tarihi wanda ba koyaushe ake samun hakan ba a wasu waƙoƙin. Wannan nazari ya dace da samun salon bayar da tarihin abin da ya faru na gumurzun maza kamar yadda aka kawo a cikin waƙar ta Sarkin Gabas a tafiyarsu Daba da irin abin  da ay biyu bayan hakan a Bunguɗu.     Muhimman Kalmomi: baka, hikima, labari, salo, da waƙa