DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.12 |Issue 1 | April 2025|
Haruna Umar Bunguɗu, Halima Adamu
Sashen Hausa na Tsangayar Ilimin Harsuna, Kwalejin Ilimi Da Ƙere-ƙere ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara
Tsakure
Makaɗa suna amfani da wani nao’in salo da ake kira salon dibilwa, a cikin waƙoƙin baka na Hausa wani salo ne na nuna gwanintar harshe da ƙwarewa ta yadda sukan kawo wata kalma da a zahiri ba ma’anarta suke nufi ba, sai su bar mai sauraron waƙar ya samar ma kansa mafita ta hanyar gano manufar, ko kuma su kawo waso zantuttukan azancin Magana wanda sai mai sauraro ya yi nasa ƙoƙarin sannan zai fahimci manufarsu. Makaɗa Abubakar Amadu Kassu Zurmi gwani ne wajen amfani da wannan salon a cikin waƙoƙinsa, don haka ne wannan muƙalar ta yi nazarin yadda ya kawo shi a cikin waƙoƙin tare da sharhantawa don amfanin manazartan waƙoƙin Hausa. Manufar wannan muƙala ita ce yin nazarin kalaman dibilwa da azancin Magana a wasu waƙoƙin Kassu tare da bayyana sautukan da mawaƙin yake amfani da su domin ƙulla zaren tunaninsa. An yi amfani da dabarar sauraren waƙoƙimsa da nazarce-nazarcen masana a matsayin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan da aka yi amfani da su a wannan muƙala. A ƙoƙarin cimma manufa an yi amfani da mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wacce ta bayyana hanyoyin da ake nazarin yadda ake nazarin waƙar baka bahaushiya (WBB). Wanda ya jagoranci wannan mazhabar shi ne Farfesa Sa’id Muhammad Gusau. Bayan kammala wannan muƙala, an an lura da da cewa Makaɗa Kassu Zurmi yana amfani da salon dibilwa da azancin Magana don nuna gwanintar harshe da kuma yin waskiya a cikin waƙoƙinsa. Zaɓaɓɓun kalmomi: Titif. ɗamrin baki, rimis, ‘Yan nalutsa, tara.