DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.35   |Issue 1 | April 2025|

Dano Balarabe Bunza, Sani Yahaya Mafara

Tsangayar Fasaha, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Abdu Gusau Polytechnic, Talata Mafara, Zamfara State

Tsakure 

An rubuta maƙalar domin a fito da salon hira da ke cikin waƙoƙin da aka ambata a sama domin tabbatar da akwai shi a cikin waƙoƙin da ake magana a kai. Salon hira na nufin tattaunawa tsakanin makaɗi da masu sauraro ko da tauraro ko kuma da wasu a cikin waƙa dangane da wata matsala ko wani shaani  da waƙa ta ƙunsa. Maƙalar ta nazarci salon hira da ke cikin waƙoƙin biyu, an kuma sami wasu nau’o’in salon hira da makaɗin ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin nasa kamar yadda ƙumshiyar takardar ta bayyana. An yi haka ta fuskar farauto waƙoƙin da sauraren su da yin nazarin su, aka saurare su da kuma tsamo salon hira a cikinsu. Maƙalar ta gano cewa, akwai nau’o’in salon hira daban-daban a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi, kuma an kawo su ɗaya bayan ɗaya tare da bayani da ingantatun misalai. An kawo misali na kowane nau’in salo da aka samu daga waƙoƙin da aka nazarta. Haka kuma, maƙalar ta gano cewa makaɗa Kassu haziƙi ne a fagen waƙa, kuma shi kaɗai ke rera waƙoƙinsa ba tare da taimakon yan amshi ba. Daga cikin nazarin da aka yi, maƙalar ta gano cewa salon hira muhimmi ne a cikin waƙoƙin baka domin yana ƙayatarwa sosai tare da jan hankulan masu sauraro dangane da abubuwan da suke gudana tsakanin jama’a a cikin waƙa.Kadadar wannan maƙala ita ce waƙoƙin biyu da aka zaɓa, wato, waƙar Nomau Namagarya da waƙar Shayi ɗan Gidan Labbo.