DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.29   |Issue 1 | April 2025|

Abdurrahman Faruk  

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina

Tsakure 

Manufar takardar ita ce yin nazari a cikin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Alhaji Kassu Zurmi. An bi hanyoyin sauraron waƙoƙin Kassu daga emfitiri (MP3) da karanta wasu littattafan masana fagen waƙar baka da fasahar labartawa wajen gudanar da wannan aiki. An ɗora wannan bincike a kan Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya ta Gusau (2014) Bayan an kammala maƙalar, sai aka gano cewa, da yawa daga cikin ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi da labartawa aka saƙa su. An kuma gano cewa, waƙoƙin Kassu masu fasalin labartawa sun fi tsawo da samun farin jinin masu sauraro. Labartattun ɗiyan waƙa sun fi waɗanda ba labartattun ba yawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kassu Zurmi.   Fitilun Kalmomi: Labartawa, waƙa, Kassu Zurmi.