DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.59     |Issue 1 | April 2025|

Maryam Bawa,   

Anas Salisu Muhammad   

Department of Hausa Language, Federal Uniɓersity of Education Kano 

Tsakure

Sarrafa harshe lamari ne mai ƙayatarwa da ke bayyana ƙwarewar harshe. Sanin harshe yana tattare da sanin nahawun harshe da yadda ake sarrafa shi. Makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi fitaccen makaɗin maza ne da yake da baiwa ta waƙa. Manufar wannan maƙala ita ce fito da sarrafa harshe da makaɗa Kassu ya yi a cikin wasu waƙoƙinsa, tare da fayyace su da misalansu domin ganin yadda sarrafa harshe yake. Maƙalar za ta yi amfani da dukkan hanyoyin biyu na bicike wato manya da ƙananan hanyoyi. A cikin hanyoyin kuwa za a yi hrarraki da karance-karancen kundaye da mujallu da litattafai duk domin samun wata gudummuwa da za ta gina wannan maƙala. Za a kuma yi amfani da hanyar ɗora aiki ta amfani da karin maganar Hausawa mai cewa “ɗan na iya wanda ya fi ɗan na koya”. Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa makaɗa Kassu tantagaryar Bahaushe ne wanda ya naƙalci harshen Hausa kuma yake sarrafa shi a cikin mafi yawan waƙoƙinsa.