DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.48 |Issue 1 | April 2025|
Abdullahi Muhammad Birnin Magaji
Gidan Rediyon Zamfara Sashen Hausa Kwalijen Fasaha da Kimiya, Gusau. (ZACAS)
Tsakure
Duk wani abu da ya shafi fasahar bayyana nagartaccen tsarin rayuwa ta mutum da kuma al’umma wadda ta shafi duniya da wadda ta shafi Lahira tana nan tule a cikin waƙoƙin baka na Hausa (Gusau, 2014). Alhaji Kassu Zurmi yana ɗaya daga cikin mawaƙan baka na Hausa, wanda Allah ya ba shi basira da hazaƙa da fasaha da hikimar naƙaltar harshen Hausa da adabi da abin da ya shafi al’adun Hausawa tun daga sana’a da muhalli da aure, da haihuwa da kuma sunayen Hausawa na kafin musulunci da kuma bayan musulunci. Don haka, Kassu Zurmi mawaƙi ne na maza, wato mafarauta da ‘yan tauri da ɓarayi, saboda haka, waƙoƙinsa ƙunshe suke da sunayen Hausawa na gargajiya tun kafin musulunci da kuma waɗanda suka samu bayan zuwan musulunci. Akwai ayyuka da dama daga masana da masu bincike a dangane da abin da ya shafi ma’anar suna da sunayen Hausawa na gargajiya da kwatanta sunayen gargajiya na Hausawa da kuma kiran sunan mutum na asali tare da laƙabin garinsu ko unguwarsu da abin da ya shafi sakaya suna na asali na Bahaushe.