DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.42     |Issue 1 | April 2025|

Musa Muhammad Labaran 

Badariyya Aliyu Alhassan 

Ɗalibi a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Tsakure 

Alamtarwa da jinsintarwa suna cikin dabarun adonta harshe waɗanda makaɗan baka na Hausa suke amfani da su wajen nannage saƙonni na yabo da zuga da kirari da zambo a cikin ɗaiɗaikun ɗiyan waƙoƙinsu, domin nuna gwanintar harshe da kwalliya a cikin waƙa. babbar manufar wannan takarda ita ce yin tarken dabarar alamtarwa da jinsintarwa a cikin wasu waƙoƙin Kassu Zurmi da fayyace muhallan da ya yi Amfani da dabarar alamtarwa ta nasaba da asali da kuma dabarar jinsintarwa ta mutuntarwa da dabbantarwa da kuma abuntarwa. An zaɓi Ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (1979, 1993, 2003, 2014 da kuma 2023) ne a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a kansa, domin ra’i ne wanda ya shimfiɗa wasu matakan nazari waɗanda ake amfani da su wajen yin nazarin dabarar alamtarwa da jinsintarwa a cikin waƙoƙin baka na Hausa. An yi amfani da nau’in bincike bi-bayani wajen bayyana wuraren da aka yi amfani da waɗannan dabaru a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi da sharhantarsu ta hanyar ƙalailaice ɗiyan waƙoƙin masu ɗauke da waɗannan dabarun jawo hankali. Binciken ya gano cewa, ba a samun dabarar abuntarwar abuntarwa a cikin waƙoƙin Kassu Zurmi. Haka kuma, bincike ya fahimci Kassu Zurmi yana yin amfani da waɗannan dabaru ne a cikin waƙoƙinsa domin koɗa wani jarumi ta hanyar yabo ko kirari ko kuma zuga domin ya tunzura zuciya kan aikata wani abu, wanda idan babu wannan zuga ko yabo, ba zai iya aikatawa ba. Fitilin Kalmomi: Tarke, Alamtarwa, jinsintarwa, ɗiya, Kassu Zurmi.