DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.39  |Issue 1 | April 2025|

Maimunatu Sulaiman, Aisha Muhammad Agigi, Bashar Abdullahi   

Department of Hausa Language, Zamfara College of Arts and Science(ZACAS)

Tsakure  

Waƙa ta baka ko rubutacciya, tamkar gyaɗa ce, sai an fasa akan san mai ƙwaya. Waƙoƙin ɓarayi da ake wa wani kallo na daban, su ma suna ɗauke da wani saƙo na musamman ta fuskar ankarar da jamaa irin dabarun da ɓarayi suke amfani da su wajen sata, domin jama’a su hankalta su kuma kiyaye. Wannan takarda da aka wa taken “Dabarun Sata a Waƙoƙin Ɓarayi na Kassu Zurmi: Koyar da Sata ko Ankararwa? Takarda ce da ta yi nazarin wasu waƙoƙin ɓarayi na Kassu Zurmi guda biyu, domin fito da saƙon da waƙoƙin suke ɗauke da su na ankarar da jama’a dabarun sata da ɓarayi suke amfani da su. An yi amfani da rubutattun bayanai da sauraron waƙoƙin mawaƙin domin fito da misalai. A ƙarshen an gano cewa akwai wasu lokuta da yanayi da ɓarayi suka fi so domin yin sata, wato kamar yanayi na damina da duhu, da kuma dare, sukan kuma yi sanɗa da dudduƙe domin kada motsin tafiyarsu ya tada mai gida.