DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.46     |Issue 1 | April 2025|

Shamsuddeen Ismail 

Aisha Yahaya Tambuwal 

Tsakure

Wannan takarda za ta bi sawun wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Alhaji Abubakar Kassu Zurmi da ya rera domin fito da tubalan gina wasu daga cikin waƙoƙinsa. Hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike sun haɗa da sauraren waƙoƙin makaɗa Musa Ɗanƙwairo a M.P da wayar salula da kuma karanta Diwanin Waƙoƙin Hausa domin zaƙulo misalan daga waƙoƙin. haka ma, an bibiyi wasu ayyuka da suke da alaƙa da wannan nazari domin samun ƙarin haske a kan yadda za a inganta wannan bincike. Ra’in da aka ɗora wannan nazari shi ne, “Ra’in Madubin Ƙyallaro Al’adu”. Ra’i ne wanda yake nuni da yadda akan yi amani da adabi ko al’ada ko harshe a matsayin madubi ko ƙyallaro al’adun al’umma kamar dai yadda Ado (2017:87) ya bayyana.