DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.53     |Issue 1 | April 2025|

Chaibou Landi 

Universite Abdou Moumouni, Niamey-Niger 

Tsakure

Wannan takarda ta bayyana irin gudummuwar da wasu daga cikin waƙoƙin Kassu Zurmi ke iya bayarwa wajen ƙirƙira, tattala da kuma adana kalmomin Hausa na fannoni daban daban na cigaban al’uma kamar su : fannin noma, tarbiya, mu’amala, wasanni, jarumataka, ds. Tattara kalmomin wanɗannan fannonin, da ma wasunsu, ta hayar kalato su daga cikin wasu daga waƙoƙin na Zurmi, da kuma fassara su zuwa harshen Faransanci kan iya taikamawa wajen bunƙasa ilimi, musamman a ƙasar da Hausa ke cigaba da fuskantar mallaka da kakagida na wasu harsunan Turai. Manufar wannan bincike ita ce, ƙoto kalmomin fannu daga waƙoƙin Kassu Zurmi ta hanyar rubuta su bisa bin umurnin ƙudirin dokar rubutun daidaitacciyar Hausa mai lamba 212 na 19 ga watan Oktoba 1999 na ofishin Ministan ilimi na Jamhuriyar Nijar. Sakamakon binciken zai taimaka sosai da muhimman kalmomi don amfani da su a fannoni daban-daban. Keɓaɓɓun kalmomi : Boda, waƙoƙin Kassu Zurmi, rumbun tsimin, kalmomin fannu, Hausa, Faransanci.