DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.32 |Issue 1 | April 2025|
Aishatu Shehu Maimota
Sashen Hausa, Kwalejin Shari’a da Ilmin Addinin Musuluncci ta Malam Aminu Kano,
Tsakure
Nazarin waƙoƙin baka na Hausa ba sabon abu ba ne duba da tarin ayyuka da aka gabatar, sai dai a kodayaushe mai nazarin kan yi ƙoƙarin zaƙulo wasu abubuwa da zummar ƙara haska wasu hikimomi da Allah ya yi wa makaɗan Hausa da ya kamata a ƙara faɗaɗa bincike a kan su. Wannan bincike an gudanar da shi ne da nufin bibiyar yadda makaɗa Abubakar Kassu Zurmi yake amfani da salon bayar da labari da na hira a waƙoƙinsa da ya yi wa ɓarayi. An gudanar da wannan bincike a kan waƙoƙi guda biyu da ya yi wa wasu ɓarayi masu suna ‘Sale na Gidan Goga’ da ‘Iro sai Mame.’ Wasu daga cikin hanyoyin da aka bi wajen gudanar da binciken sun haɗa da karanta matanin waƙoƙin da saurarar su, tare da mayar da hankali kan sauraren yadda makaɗn ke bayar da labari da yin hira a waɗannan waƙoƙi, domin su dace da manufar binciken. An kuma tattauna da wasu masana da suka yi ayyuka a kan Makaɗa Kassu Zurmi da ɗaiɗaikun jama’a da suke da sha’awar waƙoƙinsa. Muƙalar tana kan koyarwar Yahya (2016) wanda a ciki ya yi magana a kan salailan biyu da nau’insu a waƙoƙin Hausa. Daga cikin ire-iren salo da ya kawo wannan takarda ta zaɓi biyu ta binciko tare da ƙarin haske a waɗannan waƙoƙi. Daga ƙarshe wannan bincike ya gano lallai makaɗa Kassu Zurmi gwani ne na amfani da salon bayar da labari da na hira musamman a yadda aka samu hakan a waɗannan waƙoƙi biyu da aka nazarta.