DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.15  |Issue 1 | April 2025|

1Ibrahim Abdullahi Sarki Sudan, 2Nura Lawal  

1Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto 

2Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano


Tsakure            

Babbar manufar wannan takarda ita ce fito da yanayin dangantakar mata da maza, wato ‘yantauri da mafarauta da makamantansu a wasu waƙoƙin Kassu Zurmi, musamman ta la’akari da tsarin zamantakewar alaƙar maza da mata tun daga matakin ‘yanmatanci da samartaka har zuwa zamantakewar aure. Hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen tattaro bayanai da misalan ɗiyan waƙoƙin da aka yi amfani da su, sun  haɗa da sauraren wasu waƙoƙin daga  MP3 sannan aka juyar da su a rubuce. Haka kuma an tsamo wasu ɗiyan waƙoƙin daga littattafai masu ɗauke da waƙoƙin Kassu Zurmi. A wannan nazari an lura, Kassu Zurmi yana amfani da dabarun na bibiyar yanayin dangantakar soyayyar da take tsakanin jarumansa da kuma mata duk da cewa yawancin ‘yantauri da mafarauta duk matalauta ne ko kuma matsiyata kamar yadda yake ambatar su a cikin waƙoƙinsa. Har wa yau, an fahimci a wasu waƙoƙin na Kassu Zurmi, yakan nuna yadda kyakkyawar alaƙa take tsakanin mata da maza, musamman ta fuskar yadda ‘yanmata da mata suke nuna gabata da hakin kyauta da rufa asiri da bayar da shawarwari da kuma taimako ga mazajen duk da yanayinsu na fatara. A waƙoƙin na Kassu, an gano cewa, mata suna son mazaje jarumai ko da kuwa ba su da arziki, don shahara ko bajintarsu ko kuma surar jikinsu. Ashe kenan, akwai kyakkyawar alaƙa ta soyayya tsakanin mata da maza jarumai ta hanyar yin haƙuri da yanayinsu na ɗauko magana da kuma rashin yin katabus a ɓangaren hidima, musamman wadda ta shafi kuɗi. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, waƙoƙin Kassu, waƙoƙi ne da suka yi la’akari da matsayin zamantakewar mace da namiji da tabbatar da tunanin mace ba ta iya yi sai da namiji komai lalacewarsa kamar dai yadda wando ba ya tabbata a ƙugu sai da zariya.